1 Satumba 2025 - 14:45
Source: ABNA24
Juyayin Shahadar Imam Hasanul Askary As + Bidiyo

8/Rabi’ul Auwal 260h; A irin wannan rana ne shahadar Imam Hasanul Askary As Ta kasance Imami na 11 cikin jerin Imamai jagorori da Manzon Rahama Muhammad SAWA ya barwa al’ummar sa domin suyi koyi dasu don su samu tsira duniya da lahira a bayansa.

8/Rabi’ul Auwal 260h; A irin wannan rana ne shahadar Imam Hasanul Askary As Ta kasance Imami na 11 cikin jerin Imamai jagorori da Manzon Rahama Muhammad SAWA ya barwa al’ummar sa domin suyi koyi dasu don su samu tsira duniya da lahira a bayansa.

Imam Hasan As Ɗa ne ga Imamul Aliyul Hady As ana masa alkunya da Aba Muhammad ana masa lakabi da Askary wanda wannan lakabin ya samo asali ne saboda tsaron dole da hukumar lokacin ta sanya akansa da Mahaifinsa As a Samirra’a wanda alokacin wajen ya kasance sansani ne na sojojin Khalifan Abbasawa hakan ya faru kawai saboda su tsananta masa tsaro don kada ya sadu da mabiyansa da kuma lura dashi don kada a haifi Imamul Mahdy As imami na ƙarshe cikin jerin A'imma 12 As.

Matsanancin tsaron da akayi masa shiya sanya Imam ya zabi wasu wakilai domin ya rinka saduwa ta hanyar su da mabiyansa, Usman Dan Sa’id ya kasance daya daga cikin su wanda yake kula da wakilci alokacin rayuwar Imam da bayan yayi shahada kuma ya tabbata akan wannan matsayi har lokacin Gaiba Karama ta Imamul Mahdy As, wanda ya zamo shine farkon wakilai kuma Na’ibi na musamman ga Imamul Mahdy As.

Imam As ya wanzu a Samira’a shekaru 20 da wata 9 bayan ankawo shi daga madina kuma ya zauna tare da mahaifinsa acikin ta a wani yanki da ake cewa Askar, wazirin fadar Abbasawa Ahmad bin Khaqan ya siffantashi da cewa: ban ga ko sanin wani daga dangin Ali a sirri man ra’a ba kamar Hasan dan Ali ba kuma banji labarin misalin sa ba wajen kyauta da nutsuwa kamun kai kaifin hankali da karamci ga iyalansa da sauran bani Hashim ba sama dashi ba.

Imam As ya bar wasu gungu na hadisai a bangarori na tafsiri da Akhlakh da Hukunce-hukunce na Akidah da kuma wasu adduo’I.

Imam As alokacin imamancin sa yayi zamani da khalifofin abbasawa kuku Amu’utaz Almuhtady da Almu’utamad, mujarradin gayyatar Imam As da mahaifinsa daga madina da umarnin Khalifa mutawakkil zuwa Samirra shi da kanshi wani nau'i ne na tsare shi da yi masa iyaka ta rayuwa a kuntace domin su samu dammar bibiyar harkokin Imaman guda biyu duk da haka Imam ya sha wahala da takurawa da yi masa mu’alama maras dadi tare da sanya shi acikin kurkuku da gallaza masa, imam As kafin yayi shahada ya umarci mahaifiyarsa da ta tafi aikin Hajji a shekarata 259 kuma ya sanar da ita abunda zai faru dashi a shekara ta 260 sannan ya sallamawa Imamul Mahdy As dukkan abubuwan gado da suka hada harda takobi, sannan mahaifiyarsa ta fita tare da jikanta Imamul Mahdy As zuwa Makka. Imam yayi Shahada a ranar Jumaa’ah takwas ga watan rabi’ul Awwal a sirriman ra’a a gidan sa da aka binne Mahaifinsa Imamul Aliyul Hady As.

Your Comment

You are replying to: .
captcha